19 Agusta 2020 - 13:41
Shugaban Kasar Lebanon Ya Ce: Babu Batun Yin Sulhu Da Isra'ila Matukar Tana Ci Gaba Da Mamaye Wani Sashe Na Kasar Lebanon

Shugaba Micheal Aun ya kuma ce; A halin da ake ciki a yanzu ana gabatar da bincike akan hatsarin fashewar abubuwa a tashar jirgin ruwa ta Beirut, wanda majallisar koli ta shari’ar kasar ce take gudanarwa.

ABNA24 : Shugaban kasar ta Lebanin ya kuma ce ba za su kore yiyuwar afukuwar hastarin saboda dalilai daban-daban ba.

Micheal Aun bai kore cewa da akwai hannun kasashen waje ba a cikin fashewar abubuwan a tashar jirgin ruwan Beirut,amma bincike ne zai tabbatar ko kore hakan.

342/